Yi magana cikin sakewa

Rungumi wawata sabuwar hanyar sada zumunta inda aka bada fifiko akan kiyaye sirrin ka/ki fiye da yanda ka/kika taba gani a baya


"Ina amfani da Signal yau da kullum."

Edward Snowden
Masu bayyanar da almundahana da kuma masu kiyaye hokokin sirri

"I trust Signal because it’s well built, but more importantly, because of how it’s built: open source, peer reviewed, and funded entirely by grants and donations. A refreshing model for how critical services should be built."

Jack Dorsey
CEO of Twitter and Square

"A kayan aikin boye-boyen na'ura, Signal karshe ne. Kyauta ne kuma ga saukin aiki. Ina mai bada shawara cewar kowa yayi amfani dashi ko da yaushe."

Laura Poitras
Fitattun yan jarida da kuma fitattun masu shirya fina finai

"A kullum ina yabawa da irin tunani da kula da aka sa wajen tsaro da saukin amfani da wannan manhajar. Shine farkon zabina indai ina neman tsaro a hira ta.."

Bruce Schneier
Sanannen kuma fittacen mai fasahar tsaro na duniya

Mene amfanin yin amfani da Signal?

Bincika domin ka/ki gani abubuwa da suka sa hanyar isar da sakonni ta Signal ta zama hanyar sako mai sauki, mai karfi kuma mai tsaro.

Tura ba tare da rishin tsaro ba

State-of-the-art-end-to-end encryption (powered by the open source Signal Protocol) yana tabbatar da tsaron sakonninka/ki. Bamu da damar karanta sakonninka/ki, ko sauraron kiranka/ki haka ma wasu daban baza su iya karanta sakonninka/ki ko ji kiranka/ki ba. Zancen kare sirri dai ba tilas - dole ne a Signal ga ko wanne sako, ko wanne kira kuma ko da yaushe.

Fadi Komai

Tura rubutaccen sako, sakonnin murya, hotuna, , bidiyoyi, GIFs da kuma fayil a kyauta. Signal Na amfani da data din da ka/kika siya na wayarka/ki domin kauce wa biyan kudin SMS da MMS.

Yi magana cikin sakewa

Yi bayyanannen kiran murya ko bidiyo da mutane da suke kusa ko nesa a cikin kudin da bai taka kara ya karya ba.

Yi stick din sirri

Kara qayata bayanan sakon ka/ki ta hanyar tura sitikoki masu tsaro. Kaima/kema zaka/ki iya kirkira kuma ka/ki tura naka/naki sitikokin.

Yi fira a cikin group-group

Hirar rukuni na sauwake maka/ki saduwa da 'yan uwa, abokane da kuma abokan aiki.

Babu tallace-tallace Babu sa ido Babu wasa

Babu tallace-tallace, bamu da alaka da masu talla, kuma babu bincike mai ban haushi a Signal. Don haka, ka/ki mayar da hankali akan tura sakonni akan muhimmanbabubuwa da suka faru a lokuta da dama da kuma mutane da suke da muhimmanci a gurinka/ki.

Kyauta ga kowa da kowa

Signal kwamfani ce mara neman riba kuma mai zaman kanta. Bamu da wata alaka da wasu manyan kamfanonin fasaha, kuma bazamu taba zaman mallakin ko daya daga cikinsu ba. Daga gudumuwar kyauttutuka da mutane irinka/ki suka bayar akayi wannan kirkira.